Iran Ta Sami Nasara A Karar Da Ta Shigar Kan Amurka A Kodun Duniya

Iran Ta Sami Nasara A Karar Da Ta Shigar Kan Amurka A Kodun Duniya

Gwamnatin kasar Iran ta sami nasara a karar da ta shigar kan gwamnatin Amurka dangane da sake doramata takunkumai da ta yi.

A yau Laraba ce kotun duniya ta ICJ ta yanke hukunci dangane da karar da gwamnatin kasar Iran ta shigar kan Amurka a cikin watan Yulin da ya gabata. 

Kotun ta bukaci gwamnatin Amirka ta dage takunkuman da suka shifa jin kai da sifirin jiragen sama wadanda ta sake maida su bayan ficewarta daga yerjejeniyar shirin Nukliyar kasar ta Iran a cikin watan Mayu na wannan shekara.

Dukkan alkalan kotun ta duniya sun amince da hukuncin, kuma alkali Abdulqawi Ahmed Yusuf ne ya karanta hukuncin amadadin sauran alkalan Ya kuma tabbatar da cewa maida takunkuman ya sabawa yerjejeniya ta 1955 tsakanin Iran da Amurka.

Kafin haka dai shugaban Donal Trump na kasar Amurka ya bayyanan fecewarsa daga yerjejeniyar Nukliyar kasar Iran a cikin watann Mayu, sannan ya maida kashi farko na takunkuman da ta dorawa kasar a yayinda ya ce kashi na biyu na takunkuman zasu fara a cikin wata mai kamawa.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky