Iran Ta Jaddada Wajabcin Gudanar Da Bincike Kan Batun Hari Da Makamai Masu Guba A Siriya

Iran Ta Jaddada Wajabcin Gudanar Da Bincike Kan Batun Hari Da Makamai Masu Guba A Siriya

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada wajabcin kafa kwamitin bincike na kasa da kasa da zai gudanar bincike kan harin da aka kai da makamai masu guba a yankin Khun-Sheikhun na kasar Siriya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar da cewa: Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Sharif yana ci gaba da tuntubar bangarorin siyasar kasa da kasa ciki har da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da ministocin harkokin wajen kasashen Italiya, Kuwait, Turkiyya da sauransu kan matsalolin yankin gabas ta tsakiya musamman rikicin kasar Siriya.

A zantawarsa da manyan bangarorin siyasar kasa da kasar: Jawad Zarif ya jaddada wajabcin kafa wani kwamitin kasa da kasa domin gudanar da cikakken bincike domin bankado duk wani mai hannu a kaddamar da hari da makamai masu guba kan al'ummar Khun-Sheikhun da ke garin Adlib na kasar Siriya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky