Iran Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwagwarmayar Al'ummar Palasdinawa Domin Neman Yanci

Iran Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Gwagwarmayar Al'ummar Palasdinawa Domin Neman Yanci

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana ci gaba da nuna goyon bayanta ga al'ummar Palasdinu a gwagwarmayar da suke yi domin kai wa ga samun yanci daga bakin zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila.

A taron manema labarai da ya gudanar a jiya Litinin: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahroum Qasimi ya amsa bukatar kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba zata taba canja matsayinta dangane da haramtacciyar kasar Isra'ila ba, don haka matukar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tana mamaye da yankunan Palasdinwa, to wajibi ne Palasdinawa su ci gaba da gwagwarmaya domin 'yantar da kasarsu da dukkanin hakkokinsu.

Wannan furuci na kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya zo ne a matsayin amsa bukatar kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta neman kasashen musulmi su dauki matakin maida martani kan zaman da majalisar ministocin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta gudanar a gefen Masallacin Qudus a wajen da ake kira da katangar Nudba da Yahudawa suke daukan wajen da muhimmanci. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky