Iran Na Bikin Cika Shekaru 39 Da Samu Nasarar Juyin Musulunci

Iran Na Bikin Cika Shekaru 39 Da Samu Nasarar Juyin Musulunci

Yau, 11 ga watan Fabarairu, al'ummar Iran ke bikin cikar shekaru 39 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini.

Kamar yadda aka saba a kowace shekara, al'ummar kasar na gudanar jerin gwano domin nuna goyon baya ga tsarin da kasar take a kansa.

A nan birnin Tehran dubun dubatar jama'a ne ke haduwa a dandalin 'yanci na ''Azadi'', inda manyan jami'an kasar ciki har da shugaban kasar ke jawabi. 

Kamar yadda a sauran dukkanin garuruwa da manyan biranen kasar miliyoyin jama'a ke gudanar da irin wadannan taruka, tare da kara jaddada goyon bayansu ga juyin juya halin musulunci.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky