Hukumar Tsaron Iran Ta Sanar Da Kashe Dan Ta'addan Da Ya Shirya Hare Haren Tehran

Hukumar Tsaron Iran Ta Sanar Da Kashe Dan Ta'addan Da Ya Shirya Hare Haren Tehran

Ministan harkokin leken asiri na kasar Iran ya sanar da cewa an kashe dan ta'addan da ya shirya hare haren ta'addancin da aka kai wurare biyu a birnin Tehran a ranar Laraban da ta gabata.

Gidan levision na Presstv a nan Tehran ya nakalto Mahmood Aliwi yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma mkara da cewa bayan hare haren na Tehran a ranar laraban da ta gabata , dan ta'addan da ya shirya hare haren ya arce ya bar kasar, amma tare da taimakon hukumomin leken asiri na kasashen waje an kashe shi a wajen kasar a jiya Asabar. Ministna bai bayyana kasar da ta taimakawa wajen kashe dan ta'addar ba.

Mutane sama 17 suka yi shahada a hare haren da yan ta'adda 5 suka kai a majalisar dokokin kasar Iran da kuma haramin Imam Khomaini (q) a nan birnin Tehran. Sannan wasu 52 kuma suka ji rauni.

Kungiyar yan ta'adda ta Daesh ta dauki alhakin kai hare haren na Tehran. Daga karshe ministan ya kammala da cewa a cikin yan watannin da suka gabata sun sami nasara hana shirye shiryen kai harin ta'addanci hau sau 25 a duk fadin kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky