Hizbullah: 'Yan Ta'adda Na Shakar Lumfashinsu Na Karshe A Gabashin Lebanon

Hizbullah: 'Yan Ta'adda Na Shakar Lumfashinsu Na Karshe A Gabashin Lebanon

Mayakan kungiyar Hizbullah na ci gaba da killace 'yan ta'adda da suka yi saura a cikin yankin Ta'al Nisab da ke cikin gundumar Jurud Arsal a kan iyakokin Lebanon da Syria, inda dakaruna na Hizbullah suka bayar da wa'adi ga 'yan ta'addan takfiriyyah da su mika kansu da makamansu, ko kuma a murkushe su da karfin bindiga.

Dakarun na Hizbullah sun tsarkake mafi yawan yankin daga 'yan ta'addan Jabhat Nusra da suke samun goyon wasu sarakunan larabawa gami da Isra'ila, tare da mika yankunan da suka tsarkake ga rundunar sojin kasar Lebanon.

A yau ne jagoran kungiyar ta Hizbullah zai gabatar da wani jawabi da kimanin karfe 8:30 na dare agogon Beirut dangane da halin da ak ci a ci gaba da tsarkake yankunan gabashin Lebanon daga 'yan ta'addan takfiriyyah.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Prophet's birthday celebrations
We are All Zakzaky