Hizbullah Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Ta'addanci Saudiyya A Yeman

Hizbullah Ta Yi Allah Wadai Da Kisan Ta'addanci Saudiyya A Yeman

Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ta yi tofin Allah tsine kan kisan gillar da rundunar kawancen Saudiyya ta yi wa fararen hula a lardin Hudaidah da ke yammacin kasar Yamen.

Kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ta fitar da bayanin yin Allah wadai da matakin da kasar Saudiyya da kawayenta na kasashen Larabawa suka dauka na ci gaba da kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan  kasar Yamen, inda suke kashe fararen hula musamman mata da kananan yara gami da tsofaffi tare da rusa makarantu, asibitoci, wajajen tarihi da duk wani waje mai muhimmanci a kasar.

Kungiyar ta Hizbullahi ta kuma bayyana hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya gami da kawayenta suke kai wa kan kasar Yamen a matsayin laifukan yaki, don haka dole ne kungiyoyin kasa da kasa su hanzarta daukan matakan gaggawa kan irin wannan bakin zalunci na rashin dan Adamtaka.

A yammacin jiya Alhamis ne jiragen saman yakin Saudiyya da na rundunar kawancenta suka kai wasu munanan hare-haren wuce gona da iri kan sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin al-Ku'e da ke garin Addurayhimi a lardin Hudaidah, inda suka kashe fafaren hula akalla 31 da suka hada da mata da kananan yara.   


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky