Hizbullah Ta Sami Nasara A Zaben Labanon

Hizbullah Ta Sami Nasara A Zaben Labanon

Rahotanni daga kasar Labanon na nuni da cewa kungiyoyin Hibzullah da Amal da kawayensu sun sami gagarumar nasara a zaben 'yan majalisar kasar da aka gudanar a jiya Lahadi.

Rahotanni daban-daban da suke fitowa daga kasar Labanon din suna cewa jerin sunayen hadin gwiwa tsakanin Hizbullah da Amal sun lashe dukkanin kujerun 'yan majalisar da suke Kudancin Labanon bugu da kari kan wadanda suka samu a yankin Bekaa da Baalbeck-Hermel da Sidon-Jizzine da Baabda da wasu yankuna na Beirut.

Rahotanni sun ce cikin kujeru 27 na 'yan Shi'a a majalisar kasar ta Labanon, Hizbullah da Amal din sun lashe kujeru 26 bisa sakamakon farko-farko na zaben.

A wani lokaci a yau Litinin ne ake sa ran Ma'aikatar cikin gidan kasar Labanon din za ta fitar da cikakken sakamakon zaben da aka gudanar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky