Hizbullah Da Sojojin Siriya Sun Kwato Wasu Yankunan Kan Iyaka Daga Hannun 'Yan Ta'adda

Hizbullah Da Sojojin Siriya Sun Kwato Wasu Yankunan Kan Iyaka Daga Hannun 'Yan Ta'adda

Dakarun kungiyar Hizbullah da sojojin Siriya sun sami nasarar kwato wasu yankuna da kauyuka alal akalla guda 9 da suke kan iyakokin kasashen Siriya da Labanon daga hannun 'yan ta'addan kungiyar Jabhatun Nusra a hare-haren da suka kaddamar a jiya Juma'a.

Rahotanni sun ce dakarun na Hizbullah sun sami nasarar kwato yankunan da suka hada da Sahl al-Raweh, Sahr al-Haweh, Wadi Dakik, Taftanaz da kuma Wadi Zaarour Baren da suke yankin Juroud Arsal da ke wajen birnin Arsal na kasar Labanon a jiya Juma'a bayan shekara da shekaru da 'yan ta'addan Jabhatun Nusra suka yi suna rike da wajen.

Har  ila yau a yankin duwatsun Qalamoun na kasar Siriya kuwa, dakarun kungiyar ta Hizbullah sun kwato tsaunukan al-Burkan da al-Koreh Awwal, Zalil al-Haj da kuma Harf al-Sabah wadanda 'yan ta'addan suke rike da su.

A jiya Juma'a ne dai dakarun kungiyar Hizbullah din da sojojin Siriya suka kaddamar da hare-haren kwato wadannan yankuna daga hannun 'yan ta'addan wadanda suke amfani da su wajen kai hare-hare cikin kasar Siriya da kuma Labanon din lamarin da dakarun na Hizbullah suka ce ba za su taba amincewa  da hakan ba, musamman ganin cewa 'yan ta'addan sun mai da yankin na Arsal wata tungarsu da kai hare-haren ta'addanci kan yankunan da Hizbullah din suke da jama'a. Kungiyar dai ta ce ba za ta dakatar da wadannan hare-hare ba har sai sun tsarkake yankin daga dukkanin 'yan ta'addan.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni