Harin IS Ya Kashe Mutum 30 A Yayin Zaben Pakistan

Harin IS Ya Kashe Mutum 30 A Yayin Zaben Pakistan

Rahotannin daga Pakistan na cewa mutane a kalla talatin ne suka rasa rayukansu, kana wasu 30 kuma na daban suka raunana a wani harin kunar bakin wake da aka kai a kusa da wata runfar zabe dake lardin Qetta a kudu maso yammacin kasar.

Harin dai ya auku ne a daidai lokacin al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokoki a yau Laraba.

Tuni dai kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko Da'esh ta fitar da wata sanarwa a ashafin yada farfaganta na Amaq cewa ita ce ke da alhakin kai harin.

Bayanai sun ce an kai harin ne jim kadan bayan wani harin gurneti a wani ofishin zabe a lardunan Khuzdar da Baloutchistan, inda wani jami'in yan sanda guda ya mutu, wasu uku kuma suka raunana


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky