Harin bam ya hallaka mutum 10 a Rasha

Harin bam ya hallaka mutum 10 a Rasha

Mutum 10 ne suka mutu yayin da bam ya tashi a tsakanin wasu tasoshin jirgin kasa na karkashin kasa a birnin St Petersbugs na Rasha.

Shugaban hukumar yaki da ta'addanci na kasar, ya ce fashewar bam din ya shafi wani jirgin kasa tsakanin tasoshin Sennaya Ploshchad da Tekhnologichesky.

Hukumar ya ce daga bisani an gano wani bam din da bai tashi ba a wata tashar jirgin da ke kusa da wadancan.

Firai minista Dmitry Medvedev, a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook ya ce, 'harin na ta'addanci ne.'

Tuni an kaddamar da binciken ta''adanci kan lamarin, amma kuma ana wani binciken kan wasu abubuwan da za su iya zama dalilan kai harin.

Me ya faru?

Hotunan farko da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda wani jirgin kasa ya huje a tashar Tekhnologichesky Institut, aka kuma samu jikkatar mutane da dama.

Rahotannin da aka samu da farko sun nuna cewa fashwar bam biyu aka samu, daya a tashar Sennaya Ploshchad dayan kuma a tashar Tekhnologichesky Institut.

Amma hukumar yaki da ta'addanci ra kasar, daga baya ta tabbatar da cewa bam daya ne ya tashi a tsakanin tasoshin biyu da misalin karfe 11.30 agogon GMT.

Wani babban mai bincike Svetlana Petrenko ya shaida wa kafofin yada labaran Rasha cewa, matakin da direban jirgin ya dauka na ci gaba da tafiya ya matukar taimakawa wajen ceton rayuka da dama, don hakan ya sa mutane sun tsira da gaggawa.

An yi ta samun bambancin bayanai wajen yawan mutanen daabin ya rutsa da su. Amma dai a baya-bayan nan ministan lafiyar kasar Veronika Skvortsova, ya ce mutum 10 ne suka mutu, bakwai daga cikin su a take a wajen, daya a hanyar zuwa asibiti yayin da sauran kuma suka mutu a asibiti.

Mutum 37 kuma sun jikkata.

An rufe dukkan tasoshin jiragen kasa na karkashin kasa a St Petersburg, kuma jami'an tasoshin a birnin Moscow sun ce suna tsaurara matakan tsaro sosai sakamakon wannan lamari.

Me ya jawo harin?

Shugaban hukumar yaki da ta'addanci Andrei Przhezdomsky, ya ce wani abu ne da ba a fayyace ko mene ne ba ya fashe, amma har yanzu ba a gano musabbabin lamarin ba.

Shugaba Vladimir Putin ya ce, ana binciken duk abin da ake zaton shi ne sababi, da suka hada da ta'addanci. Ya je birnin na St Petersburg a lokacin da abin ya faru, a cewar mai magana da yawunsa Dmitry Peskov.

A yayin wata ganawa da sugaban kasar Belarus, Mista Putin ya ce, "Tuni na yi magana da shugaban ayyuka na musamman, suna kokarin gano abin da ya jawo harin."

Gano wani bam din da aka yi a wata tashar jirgin kasa ta Ploshchad Vosstaniya, ya nuna cewa da gangan aka kai harin, kuma rahotanni sun ce an dasa bam din nea cikin wani karamin akwati da aka bar shi a cikin jirgin kasan.

Ba a saba ganin irin haka ba

Tashar jiragen birnin St Petersburg ita ce ta 19 da aka fi yawan hada-hada a duniya, inda ake samun fasinjoji fiye da miliyan biyu a duk rana, amma ba a taba kai hari ba a baya.

Amma an sha kai hare-hare cibiyoyin sufuri da dama na Rasha. A shekarar 2010 ma mutum 38 ne suka mutu a wasu hare-haren kunar wake biyu da aka kai wata tashar jirgi a birnin Moscow.

Shekara guda bayan nan wani bam din ya tashi a wani jirgin kasa mai tsananin gudu da ke tafiya daga Moscow zuwa St Petersburg, inda mutum 27 suka mutu, 130 kuma suka jikkata.

Kungiyar IS ta dauki alhakin dukkan hare-haren a wancan lokaci.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni