Gwamnatin Tunusiya Ta Yi Watsi Da Batun Kulla Alaka Da HK. Isra'ila

Gwamnatin Tunusiya Ta Yi Watsi Da Batun Kulla Alaka Da HK. Isra'ila

Firayi ministan kasar Tunusiya, Youssef Chahed, yayi watsi da batun kyautata alaka tsakanin kasar Tunusiya da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Kafar watsa labaran Sputnik ta kasar Rasha ta bayyana cewar firayi ministan kasar Tunusiyan ya bayyana hakan ne a jawabin da yayi a gaban 'yan majalisar kasar inda ya yi watsi da magaganun da wasu suke yi na cewa gwamnatinsa na kokarin kyautatata alaka da HKI.

Firayi minista Youssef Chahed ya ce matsayar gwamnatinsa na ci gaba da goyon bayan al'ummar Palastinu har sai sun kwato hakkokinsu tana nan daram.

Cikin 'yan kwanakin nan dai gwamnatin firayi ministan Chahed din tana fuskantar suka ne sakamakon nada Rene Trabelsi, wani bayahude, a matsayin ministan yawon shakatawa na kasar, lamarin da ya firayi ministan ya ce Mr. Trabelsi din dan kasar Tunusiya ne don haka yana da hakkin da kowane dan kasar yake da shi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky