Gwamnatin taraiyar Najeriya zata kulle Asusun Saraki Da Dogara:

Gwamnatin taraiyar Najeriya zata kulle Asusun Saraki Da Dogara:

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar jam'iyyun Najeriya wato National Unity Party (NUP), a turance Mr. Perry Opara, ya bayyana wa manema Labarai a madadin Sauran jam'iyyu 45 cewa suna da Bayanin sirri wanda yake kunshe da sakon shirin da a ke yi na garkame Asusun shugaban majalissar Dattaw Abubakar Bukola Saraki da kuma Shugaban majalissar wakilai yakubu Dogara

A cikin Rahoton Shugaban jam'iyun Mr. Opara ya bayyana cewa a kwai wadan da suka dage kan cewa koda  karfin tuwo Ko na mulki sai sun kassara Saraki da Dogara, kuma hakan ya sabawa dokar kasa cewar opara.


Yace bazasu zura ido suna ganin  wasu 'yan siyasa don ganin mulki yana hannunsu su rika ciwa kowa mutunci hakan  yaba dokar kasa, yace dokar kasa  tabawa kowanne dan siyasa dama ya fita daga wata jam'iya middin yaga ana yimasa ba daidai ba.


Opara yacegaba da cewa ni  bana goyon bayan kowanne dan siyasa kuma duk Wanda yayi wani abu sabanin dokar kasa  to bazasu zura ido suna kallo ba.


Daga karshe yace wadanda suka samu matsayi a siyasance suji tsoron Allah su daina nuna san zuciyarsu, don ganin wani ba a jam'iyarsu yake ba, yace basa goyon bayan rufe asusun saraki da dogara.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky