Gwamnatin Masar Ta Jaddada Matsayinta Na Taimakawa Iraqi Kan Yaki Da Ta'addanci

Gwamnatin Masar Ta Jaddada Matsayinta Na Taimakawa Iraqi Kan Yaki Da Ta'addanci

Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi ya kara jaddada matsayin gwamnatinsa na tallafa wa kasar Iraqi a yakin da take yi da yan ta'adda.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Sisi yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacin da yake maraba da Priministan kasar Iraqi Haidar Abadi wanda ya kai ziyarar aiki a kasarsa. Shugaban ya ci gwamnatinsa har'ila yau tana goyon bayan dunkulelliyar kasar Iraqi.

Banda haka shugaba Abdulfata Sisi ya taya Hardar Abadi murna kan irin nasororin da sojojin kasar suke samu kan kungiyoyin yan ta'adda da kuma wadanda suke kokarin bellewa daga kasar.

A nashi bangaren Priministan kasar Iraqi Haidar Abadi ya bukaci karfafa dangantaka tsakanin kasashen Iraqi da Masar, ya kuma kara da cewa zasu yi aiki tare da tabbatar da tsaron yankin da kuma zaman lafiya, ci gaba da kuma hadin kai tsakanin kasashen yankin.

Kafin ziyararsa zuwa kasar Masar Dai Haidar Abadi ya ziyarci kasar Saudia inda a can ma batun yaki da ta'addancin ne ya mamaye tattaunawarsu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky