Gobara A Ginin Babban Bankin Najariya

Gobara A Ginin Babban Bankin Najariya

An yi gobara a cikin babban bankin tarayyar Nigeria a jiya Talata duk tare da kokarin da majiyar bankin ta yi na nuna cewa hayaki ne kawai a dakunan injin bada wutan lantarki na bankin.

Jaridar Primuim times ta nNajeriya ta ce kakakin babban bankin Isaac Okorafor ya aikata mata sako a jiya da yamma kan cewa hayaki ne kawai ya tashi a daya daga cikin dakunan ingin bada wutan lantarki na bankin, amma ba gobara bace, don haka tuna an shawa matsalar kuma ayyuka suna tafiya a bankin kamar yadda aka saba.

Amma majiyar jami'an gwana-gwana masu kashe gobara a Abuja sun tabbatar da cewa gobare ce ta kama daya daga dakunan injin bada wutan lantarki na bankin, kuma sun sami sakon neman taimakon gaggawa da misalin karfe 6.38 na yamma, sun kuma sami nasarar kashe gobatar a cikin mintuna 30.

Kakakin Babban bankin ya kara da cewa ginin bankin yana da tsarin sanarda aukuwan hatsari mai aiki da kansa (Automatic) don haka ne aka ji karar wadannan kayakin aiki a lokacinda suka sunsuni hayaki.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky