Girgiza Kasa Ta Yi Ajalin Mutane Da Dama A Iran

Girgiza Kasa Ta Yi Ajalin Mutane Da Dama A Iran

Wata mummunar girgiza kasa mai karfin maki 7.6 a ma'aunin rishta data abkawa yankunan dake iyaka tsakanin kasashen Iran da Irak ta yi ajalin mutane sama da 300

Alkalumem da hukumar agajin gaggawa ta Iran ta fitar ya ce girgiza kasar  ta yi sanadin rasa rayukan mutane sama da 300 a yayin da adadin wadanda suka raunana ya haura 1,800 a yankin Kermanshah daye yammacin kasar.

Bayanai sun ce an ji girgizar kasar har cikin biranen Tehran da Bagadaza da kuwa wasu yankuna dake arewa maso gabashin Iraki kusa da birnin Kurdawa na Halabja da Turkiyya da Israi'la da kuma Kuwai.

A cewar Ali Moradi shugaban cibiyar kula da girgiza kasa ta Iran, girgizar kasar data auku da misalin karfe 9h48 na dare agogo wurin ta hadassa tsagewar kasa mai zurfin  kilomita 11.

Tuni dai jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya isar da sakon ta'aziyarsa da kuma juyayi ga wadanda iftila'in ya rusa da su.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni