Ganawar Shugaba Rauhani Da Shugaban Hukumar IAEA A Vienna

Ganawar Shugaba Rauhani Da Shugaban Hukumar IAEA A Vienna

A ziyarar da shugaba Rauhani ya kai kasar Austria, bayan ganawa da manyan jami'an gwamnatin kasar, daya bangaren kuma ya gana da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA Yukiya Amano

A yayin ganawar, Amano ya tabbatar wa Rauhani da cewa, hukumar IAEA tana nan kan bakanta na yin riko da yarjejeniyar nukiliya da aka cimmawa tare da Iran, kuma hukumar tana ci gaba da yin aikinta na sanya ido a kan shirin Iran, inda ya kara tabbatar da cewa mutunta wannan yarjejeniya daga dukkanin bangarori shi kadai ne mafita.

A nasa bangaren shugaba Rauhani ya bayyana cewa, sun gudanar da doguwar tattaunawa tare da manyan jami'an hukumar IAEA, kuma rahotannin da hukumar suka fitar kan cewa Iran tana yin aiki da yarjejeniyar da aka cimmawa tare da ita, babban dalili ne da ke tabbatar da cewa duk wanda ya fita daga yarjejeniyar shi ne ya saba wa doka da ka'ida ta kasa da kasa.

Rauhani ya kara da cewa, Iran za ta ci gaba da mutunta wannan yarjejeniya da yin aiki da ita, matukar dai hakan zai kare maslaharta, amma a lokacin da bangarorin yarjejeniyar suka kasa kare maslahar Iran, to a lokacin za ta sake yin nazari kan wannan yarjejeniya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky