Faransa Da Masar Sun Bukaci Da A Kawo Karshen Rikici A Gabas Ta Tsakiya

Faransa Da Masar Sun Bukaci Da A Kawo Karshen Rikici A Gabas Ta Tsakiya

Shugabannin kasashen Masar da Faransa sun tattauna batun Palasdinu da kasashen Libiya da Siriya tare da jaddada bukatar daukan matakan warware rikicin yankin gabas ta tsakiya.

A zantawar da ta gudana ta hanyar wayar tarho tsakanin shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da takwararsa na kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi sun tattauna batun matsalar Palasdinu tare da hanzarta daukan matakan rage irin tarin matsaloli da al'ummar yankin Zirin Gaza suke ciki ta hanyar hanzarta aikewa da kayayyakin jin kai.

Har ila yau shugabannin kasashen biyu sun jaddada bukatar daukan matakin taimakawa duk wani kokarin kawo karshen tashe-tashen hankula da dambaruwar siyasa a kasar Libiya musamman tallafawa wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Libiya kan irin gagarumin kokarin da yake yi na ganin an kai ga samun nasarar shawo kan matsalolin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky