Erdogan Na Ziyarar Aiki A Iran

Erdogan Na Ziyarar Aiki A Iran

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya fara wata ziyara aiki a nan birnin Tehran na Jamhuriya musulinci ta Iran, inda ya gana da takwaransa na Iran din Hassan Rohani.

Bangarorin biyu za su tattauna kan batutuwan da suka shafi huldar dake tsakanin kasashen biyu da ma wasu batutuwa da suka shafi yankin dama na kasa da kasa.

Tunda farko dai an ce bangarorin biyu zasu tattauna batun zaben raba gardama na yankin Kurdistan na kasar Iraki.

Dama dai kafin hakan kasashen Turkiyya Da Iran sun sanar da karfafa matakan soji akan iyakokinsu, bayan wata ziyara da babban hafsan sojin Turkiyyar ya kawo a nan Tehran kwanaki biyu da suka gabata.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky