Erdogan Da Salman Sun Tattauna Ta Wayar Tarho kan Kashoggi

Erdogan Da Salman Sun Tattauna Ta Wayar Tarho kan Kashoggi

Shugabannin Saudiyya da Turkiyya sun tattauna ta wayar tarho kan batan dan jarida Jamal Khashoggi da ake zargin an kashe shi a karamin ofishin jakadancin Saudiyar na Istambul a farkon watan nan.

Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiya (Wass) ya habarta cewa a daren jiya lahadi sarki Salman bn Abdul-aziz na Saudiya ya tattaunawa da shugaban  kasar Turkiya Rajab Tayyib Erdogan kan fitaccen dan jarida na  kasar Saudiyya da aka zargin mahukuntan kasar sun kashe shi a karamin ofishin jakadancin kasar dake birnin Intambul na Turkiya.

Sarki Salman Bin Abdul'ziz ya tabbatar da kyakkyawar huldar da ke tsakanin kasarsa da Turkiyya, inda ya bukaci ci gaba da kiyaye da kuma bunkasa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare Shugaba Erdogan ya yabawa Sarki Salam na Saudiya kan muahimancin da ya bawa alakar dake tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kasarsa za tayi nata kokari wajen kare alakar dake tsakanin kasashen biyu, to sai dai ya bukaci hadin kan na hukumomin saudiyar wajen gudanar da bincike kan abin da ya faru da fitaccen dan jaridan Jamal Khashoggi a karamin ofishin Jakadancin Saudiya dake birnin Istambul.

Jamal Khashoggi dai fitaccen dan jarida na  kasar Saudiyya, wanda kuma ya yi ayyuka da manyan cibiyoyi a kasar, amma daga bisani ya rika sukar salon siyasar yarima Bin Salman, kamar yadda yake sukar yakin da Saudiyya take kaddamarwa kan kasar Yemen.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky