Dr Ruhani: Amurka Tana Kaskanta Kanta Saboda Sabawa Ka'idojin Kasa Da Kasa

Dr Ruhani: Amurka Tana Kaskanta Kanta Saboda Sabawa Ka'idojin Kasa Da Kasa

Shugaban Hassan Ruhani na kasar Iran ya bayyan jawabin da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi a babban zauren majalisar dinkin duniya a jiya Talata, jawabin ya kaskanta kasar Amurka ne a gaban kasashen duniya

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar a babban zauren MDD a dozu dazun nan, ya kuma kara da cewa yerjejeniyar shirin nukliyar kasar Iran da ta cimma da manya manyan kasashen duniya 5+1 a shekara ta 2015 yerjejeniya ce ta kasa da kasa harma komitin tsaro na MDD ya maida shi kuduri mai lamba 2231 don haka karyata daga bangaren Amurka ita kadai zata cutu.

A wani bangare na jawabinsa shugaba Ruhani mutane kasar Iran basu bukaci wani abu fiye da adalci da kuma 'yencin da samun ci gaba ba. Don haka ba zata fara karya alkawarin da ta dauka da wadan nan kasashe ba amma kuma idan sauran bangarorin suka karya nasu alkawarin Iran zata maida martanin da ya dace.

Dangane da matsalolin kasashen Yemen Bahrai, Afganistan Myanmar da Afganistan kuma, shugaban ya ce kada kasashen da suke da hannu wajen jefa su cikin yaki da tashe tashen hankula kada su zaci cewa  zasu zauna cikin zaman lafiya da ci gaba na lokaci mai tsawo ba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky