Dakarun Kare Juyi Na Iran Za Su Kara Tura Kwararrun Harkar Soji Zuwa Siriya

Dakarun Kare Juyi Na Iran Za Su Kara Tura Kwararrun Harkar Soji Zuwa Siriya

Kwamandan sojin kasa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran Birgediya Janar Muhammad Pakpour ya bayyana cewar dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun tura kwararru kan harkokin soji zuwa Siriya don taimakawa sojojin kasar fadar da suke yi da ta'addanci kuma a nan gaba ma za su ci gaba da turawa.

Janar Pakpour, Kwamandan sojin kasa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da kamfanin dillancin labaran Fars na Iran inda ya ce makiyan al'umma suna da wasu tsare-tsare da suka shirya don cutar da al'ummar Siriya, don haka ba za mu iya rufe ido kan hakan ba a matsayin kasar Siriya na daya daga cikin sansanonin 'yan gwagwarmaya.

Don haka sai ya ce Iran za ta ci gaba da tura irin wadannan kwararru nata bisa bukatar da gwamnatin Siriya ta yi mata don taimaka mata a fadar da take yi da 'yan ta'addan da aka tura su kasar Siriya da nufin dagula lamurra a kasar.

Kasashen da suke goyon bayan ayyukan ta'addancin da ke faruwa a kasar Siriya suna zargin Iran da tura dakarunta kasar alhali kuwa dukkanin kwararru harkar soji da Iran take turawa Siriyan tana yin hakan ne bisa gayyatar da gwamnatin Siriyan ta yi musu.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky