Dakarun Juyin Juya Halin Na Iran Sun Kashe Way Yan Ta'adda Uku

Dakarun Juyin Juya Halin Na Iran Sun Kashe Way Yan Ta'adda Uku

Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun kashe yan ta'adda ukku a kan iyakar kasar da kasar Iraki sun kuma gano makamai da dama a wajensu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa dakarun juyin juya halin sun gano wata tawagar yan ta'adda masu adawa da JMI wadanda suka ketara kan iyakar kasar da kasar Iraqi a lardin Kermansha kuma sun fafata da su har suka kashe ukku daga cikinsu a yayinda dayansu ya ji rauni. Har'ila yau labarin ya bayyana cewa daya daga cikin dakarun juyin juyin juya halin musulunci ya yi shahada.

Labarin ya kara da cewa tawagar yan ta'addan tana nufin kai hare hare a cikin kasar, amma dakarun suka shawo kansu kafin su aikwatar da mummunar anniyarsu. A cikin watan yunin da ya gabata ba dakarun Quds Brigate sun kashe wasu yan ta'addan ukku a wani fafatawa da suka yi a kudu maso yammacin kasar


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky