Buhari zai Kai Ziyarar Jajantawa Mutanen Fulato

Buhari zai Kai Ziyarar Jajantawa Mutanen Fulato

Rahotanni daga Najeriya na cewa akwai yiwuwar shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Filato a yau Talata don jajanta wa al’ummarta sakamakon rikicin baya-bayan nan da ya lakume rayukan mutane kusan 100

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta rawaito cewa, shugaba Buhari zai yada zango a Filato bayan ya baro birnin Calabar da ke jihar Cross Rivers a yammacin yau.

A wannan safiya ne shugaba Buhari ya kama hanyarsa ta zuwa Calabar daga birnin Abuja don kaddamar da wasu ayyukan gwamnati a jihar.

A jiya ne mataimakin shugaban, Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Filato saboda wannan ibtila’in da ya afka ma ta.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky