Buhari Ya Gana Da Trump A Kan Yaki Da Ta'addanci

Buhari Ya Gana Da Trump A Kan Yaki Da Ta'addanci

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya gana da kuma tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump kan batutuwa daban-daban musamman kan batun fada da ta'addanci inda shugaban Amurka ya yaba wa shugaba Buharin kan nasarorin da gwamnatinsa take samu a fada da ta'addancin da take yi.

Shugabannin biyu dai sun gana ne a fadar White House ta Amurka a ci gaba da ziyarar da shugaba Buharin yake yi a Amurka bisa gayyatar da shugaban Amurkan yayi masa na ya ziyarci Amurkan don samun damar tattaunawa kan batutuwa da suka shafi batun tsaro, tattalin arziki da dai sauransu.

A wata ganawa da suka yi da manema labarai, shugaba Buharin ya gode wa Amurka kan irin taimakon da take ba wa Nijeriya a fagen fada da kungiyar ta'addancin nan ta Boko Haram da kuma amincewar da ta yi na ta sayar wa Nijeriya da wasu jiragen yaki, kamar yadda kuma ya bukaci gwamnatin Amurkan da ta taimaka wa Nijeriya din wajen kwato makudan kudaden da wasu 'yan siyasar Nijeriyan suka sace daga asusun kasar da kuma jibge su a Amurkan.

Shi ma a nasa bangaren shugaban Amurkan Donald Trump ya yabawa shugaba Buhari kan yadda yake yaki da ta'addanci a kasarsa yana mai cewa Amurka za ta ci gaba da aiki tare da Nijeriya domin magance wannan matsala, sai dai ya nuna damuwarsa dangane da kashe-kashe da ke faruwa a Nijeriya musamman mabiya addinin Kirista wanda ya ce Amurka za ta ci gaba da aiki don shawo kan matsalar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky