Buhari Ya Gana Da Shugabannin Majalisa

Buhari Ya Gana Da Shugabannin Majalisa

A wani abin da ake gani a matsayin kokarin dinke barakar da ta kunno kai tsakanin fadar shugaban Nijeriya da majalisun kasar, shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriyar ya gana da shugabannin majalisun tarayyar kasar su biyu a daren jiya.

Rahotanni sun ce a daren jiya Alhamis ne dai shugaba Muhammadu Buharin yayi wata ganawa ta musamman da shugaban majalisar dattawan Bukola Saraki da ta wakilai Yakubu Dogara bugu don tattaunawa batutuwa daban-daban da suka shafi bangarori biyu da kuma kasar baki daya.

Duk da cewa fadar shugaban kasar ba ta yi cikakken bayani dangane da ganawar ba, to amma dai majiyoyi da dama suna ganin ganawar tana da alaka ne da rikicin da ta kunno kai tsakanin fadar shugaban kasar da majalisar biyo bayan kin amincewa da shugaba Buharin yayi ya sanya hannu kan wasu dokoki da 'yan majalisar suka gabatar masa da suka hada da kafa dakarun Peace Corp da kuma batun sauya jadawalin lokacin zabe a kasar.

Kin sanya hannu da shugaban yayi dai ya janyo kace nace musamman tsakanin 'yan majalisar inda wasu suke barazanar amfani da karfin da doka ta ba su na yin gaba gadi wajen kafa dokar matukar shugaban ya ki sanya hannu lamarin da wasu masana harkokin shari'a a kasar suke ganin ba su da hurumin yin hakan.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky