Buhari ya gana da dalibai 107 da aka sako

Buhari ya gana da dalibai 107 da aka sako

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi da aka sako ranar Laraba

Ya yi ganawar ce a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

A jawabinsa lokacin ganawar, Shugaba Buhari ya ce "Ina farin cikin sanar da 'yan Najeriya da abokanmu na kasashen waje da kuma wadanda muke hada gwiwa da su cewa an saki ba tare da sharadi ba dalibai 107, 105 daga cikinsu 'yan matan makarantar Dapchi da kuma mutum biyu da a baya aka sace."

Ya kara da cewa sakin matan - bayan da ya umarci jami'an tsaron kasar su tabbatar babu abin da ya same su - abin farin ciki ne.

   Shugaba Buhari ya sha alwashin ganin an sako daliba daya da ta rage a hannun mayakan Boko Haram da kuma 'yan matan Chibok da aka sace tun 2014.

Ranar Laraba aka sako 'yan matan, wadanda aka sace a watan jiya.

Mahaifin daya daga cikin 'yan matan, Kundili Bukar, ya gaya wa BBC cewa wasu mutane da ake tsammani 'yan Boko Haram ne suka mayar da matan a motoci

A cewarsa, sun ajiye su ne kawai suka tafi kuma 'yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.

Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam'iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan domin cimma wata bukata ta siyasa.

Sai dai APC ta musanta zargin.

A watan jiya aka sace matan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami'an tsaron Najeriya.

A wancan lokacin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace 'yan matan a matsayin wani bala'i da ya shafi kasar baki daya.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni