Buhari ya amince da fitar da biliyan N10bn domin biyan diyya ga mutanen Filato da rikici ya shafa

A jiya, Alhamis, Shugaba Buhari ya bayyana cewar ya amince da fitar da biliyan N10bn da za a yi amfani da ita domin gyara tare da taimakon al’ummar jihar Filato da rikicin baya-bayan nan ya shafa.

A ranar Asabar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari tare da kashe mutane fiye da 86 a yayin da suke hanyar su ta dawowa daga wurin wata jana’iza.

Tun a ranar Litinin ne shugaba Buhari ya yi tir da kashe-kashen rayukan da aka yin a ranar Asabar a jihar Filato tare da daukan alkawarin gurfanar da duk masu hannu a ciki. Kazalika ya ziyarci yankin da rikicin ya shafa a jihar.

A shafinsa dake kafar sada zumunta ta Tuwita (@NGRpresident), shugaba Buhari ya bayyana abubuwa 7 da zai aiwatar domin kare afkuwar irin wadannan hare-hare da suka dade suna faruwa a karamar hukumar Barkin-Ladi da Riyom a jihar Filato.

“An ware biliyan N10bn domin gyarawa jama’a muhallinsu da kuma basu agaji kamar yadda aka yiwa mutanen jihar Nasarawa da Benuwe da rikici ya shafa,” a cewar fadar shugaba Buhari.

Fadar ta shugaban kasa ta kara da cewar, an aike da jirgin sama mai saukar ungulu da wasu manayan motoci masu dauke da makamai na hukumar ‘yan sanda zuwa ta Filato domin murkushe ‘yan ta’adda da aiyukan ta’addanci a jihar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky