Boko Haram Ta Kai Hari A Maiduguri

Boko Haram Ta Kai Hari A Maiduguri

Rahotannin daga Najeriya na cewa mutane a kalla 18 ne suka rasa rayukansu kana wasu 84 suka jikkata a wani hari da ake kyautata zaton na mayakan boko haram ne.

An dai kai harin ne da yammacin jiya a cewar hukumar kula da agajin gaggawa ta NEMA a yankin, wacce ta tabbatar da lamarin.

An dai kai harin ne a unguwannin ale Shuwa da Bale Kura dake kewayen birnin na Maiduguri, kamar yadda wani jami'an hukumar ta NEMA  mai suna Bello Dambatto ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaren AFP.

Jami'an ya ce galibin mutenen sun mutu ne a musayar wuta tsakanin sojoji da 'yan bindigan.

Wasu bayannai na daban sun ce an kuma kashe wasu 'yan kunar bakin wake biyu a daidai lokacin da suke kokarin tarwatsa kansu a unguwar Alikaranti,.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky