Boko Haram Sun Kai Harin Kunar Bakin Wake A Konduga

Boko Haram Sun Kai Harin Kunar Bakin Wake A Konduga

Yan kungiyar Boko Haram suka kai harin kunar bakin wakin a garin Konduga na jahar Borno dake shiyar Arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu 'yan kato da gora 5.

Rahotanni dake fitowa daga Najeriya sun tabbatar da kai hari a  ajiya Talatar a wani wurin bincike da ke a mafitar birnin Konduga mai nisan kilo mita 35 da Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Bayan hasarar raykan da aka samu, wasu mutane biyar na daban  kuma sun jikkata bayan da dan kunar bakin waken ya tarwatsa kan shi a cewar mai magana da yawun hukumar agaji ta NEMA  Abdukadir Ibrahim  a  Najeriya.

Kimanin makonni biyu da suka gabata ma dai, wasu tagwayen hare-haren da aka kai a cikin wani masallaci a jihar Adamawa, sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 86 yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka.

Jihar Borno dai ta kasance jihar da tafi fuskantar ta'addanci kungiyar Boko haram a Najeriya, kuma daga shekarar 2009 zuwa hare-haren kungiyar boko haram din ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu 20 da kuma raba wasu sama da miliyan biyu da dubu 600 da mahalinsu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky