Bin Salman: Ko Dai Falastinawa Su Amince Da Sulhu Da Isra'ila Ko Kuma Su Rufe Bakinsu

Bin Salman: Ko Dai Falastinawa Su Amince Da Sulhu Da Isra'ila Ko Kuma Su Rufe Bakinsu

Tashar talabijin ta 10 ta Haramtacciyar kasar Isra'ila ta bayar da rahoton cewa, a ziyarar da ya kai a kwanakin baya a kasar Amurka, saurayin yariman Saudiyya mai jiran gadon sarautar kasar Muhammad Bin Salman, ya gargadi Falastinawa da cewa, ko dai su amince su yi sulhu da Isra'ila, ko kuma su rufe bakunansu su daina magana.

A lokacin da tashar ta Isra'ila ta bayar da wannan rahoto a daren jiya, ta kuma zanta kai tsaye da wani fitaccen masharhanci bayahude mai suna Barack Rabid, wanda ya bayyana cewa a cikin shekaru 40 da suka gabata, babu wani shugaba daga cikin shugabannin larabawa da sarakunansu, wanda ya farantawa Isra'ila da ma yahudawa baki daya kamar Bin Salman.

Rabid ya ce Bin Salman ya tabbatar da amincewarsa da kafa dalaular yahudawa ta Isra'ila, kamar yadda kuma ya bayyana lamarin Palastinu  ko Palastinawa da cewa ba shi ne ke da muhimmanci  a wurinsa ba, kamar yadda kuma ya bayyana cewa dole ne Isra'ila da Saudiyya suka hada karfi tare domin su ga bayan Iran, da ma sauran kalamai masu faranta rai ga Isra'ila da Bin Salman ya yi a cikin 'yan lokutan nan.

Tun kafin furucin da Trump ya yi na amincewa da Quds a matsayin babban birnin Isra'ila, gwamnatin Palastinawa ta bayyana cewa, Mahmud Abbas Abu Mazin ya fuskanci matsin lamaba daga Muhammad Bin Salman, kan cewa dole ne ya amince da kudirin na Donald Trumpna mayar birnin Quds ya zama babban birnin Isra'ila, su kuma Falastinawa su mayar da garin Abu Dis a matsayin babban birninsu, lamarin da Falastinawan suka ki amincewa da shi.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky