Ayatullah,Iran Ba Za Ta Taba Mika Wuya Ga Mulkin Kama-Karyar ba

Ayatullah,Iran Ba Za Ta Taba Mika Wuya Ga Mulkin Kama-Karyar ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta taba kuma ba za ta taba mika kai ga mulkin kama-karya na ma'abota girman kai, yana mai cewa a halin yanzu Iran tana tsaya da kafafunta kyam sama da shekarun baya.

Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne a jawabin da ya yi da safiyar yau wajen bikin tabbatar da shugaba Hasan Ruhani a matsayin shugaban kasar Iran karo na 12, inda ya ce makiya sun ci gaba da matsin lamba da kulla makirce-makirce wa Iran, don haka wajibi ne al'ummar Iran da jami'an kasar su zamanto a farke. Jagoran ya ci gaba da cewa jami'an kasar Iran sun san yadda za su tinkari wadannan makirce-makirce ba tare da tsoho ba.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Wajibi ne jami'an gwamnati su yi la'akari da abubuwa uku, na farko yanayin tattalin arziki da yanayin rayuwar mutane, sannan su yi kokari wajen kyautata alakarsu da sauran kasashen duniya, na uku kuma su tsaya kyam wajen tinkarar girman kan ma'abota girman kan duniya.

A safiyar yau ne dai ne aka gudanar da bikin tabbatar da shugaba Ruhanin a karo na biyu na shugabancinsa. A bisa kundin tsarin mulkin Iran duk shugaban kasa da aka zaba yana bukatar amincewar Jagoran juyin juya halin Musulunci kafin yayi rantsuwar kama aiki a gaban majalisar dokokin kasar.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky