Ayatullahi Khamna'i Ya Jinjina ma Kungiyar Kwallon Kafa Ta Iran

Ayatullahi Khamna'i Ya Jinjina ma Kungiyar Kwallon Kafa Ta Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jinjinawa 'yan kungiyar kwallon kafa ta kasar sakamakon irin bajintar da suka nuna a yayin gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da ake gudanarwa a kasar Rasha.

Jagoran ya  isar da sakon jinjinawar tasa ne ta hannun ministan wasanni da matasa na kasar Iran din inda jagoran ya bayyana wa 'yan kungiyar kwallon kafa ta Iran cewa: Kun din nan kun dawo gida cikin nasara da daukaka, yana mai musu fatan alheri da samun nasara a nan gaba.

A jiya ne dai kungiyar kwallon kafa ta Iran din ta buga wasanta na karshe a gasar cin kofin duniya din da kungiyar kwallon kafa ta kasar Portugal inda suka yi kunnen doki daya da daya. Duk da cewa wannan sakamakon ya sanya an cire Iran daga gasar sai dai kuma an jinjina musu da irin wasan da suka yi jiya din wanda ba wanda yayi tsammanin za su yi hakan.

Iran dai ta zo ta uku ne a rukuninsu da maki hudu cikin wasanni ukun da ta yi inda ta ci kasar Moroko, ta yi kunnen doki da Portugal sannan kuma kasar Spain ta ci ta da kwallo guda.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky