Ayatullahi Khamenei: Harin Ta'addancin Tehran Ba Zai Tasiri Al'ummar Iran Ba

Ayatullahi Khamenei:  Harin Ta'addancin Tehran Ba Zai Tasiri Al'ummar Iran Ba

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar koda wasa harin ta'addancin da aka kai birnin Tehran ba zai raunana gwiwan al'ummar Iran wajen fuskantar duk wata barazana ba, yana mai jaddada cewar da yardar Allah za a tumbuke tushen ta'addanci.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da dubun dubatan daliban jami'oin Iran a jiya Laraba inda yayin da yake magana kan harin ta'addancin da wasu 'yan ta'adda suka kai wani bangare na Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran da kuma mashigar hubbaren marigayi Imam Khumaini (r.a) inda ya ce: Al'ummar Iran dai sun kama tafarkin ci gaba. Don haka wannan lamari da ya faru a yau (wato harin ta'addancin), koda wasa ba zai yi tasiri iradar al'ummar Iran. Sun gaza ainun su yi tasiri cikin karfin gwiwan al'umma da kuma jami'an kasar Iran.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa idan da a ce Iran ba ta tsaya kyam wajen fada da 'yan ta'addan a wasu kasashen yankin nan ba, to da kuwa ta ci gaba da fuskantar  irin wadannan hare-haren yana mai bayyana kyakkyawan fatan cewar da yardar Allah za a kawo karshen ayyukan ta'addancin.

A wani bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya sake jaddada matsayar Iran na tsaya kyam wajen fada da 'yan mulkin mallaka na wannan zamanin, don haka ya kirayi daliban jami'an da su kasance a sahun gaba-gaba na wannan fada da kuma kin amincewa da mulkin mallakar wasu 'yan tsirarun kasashe ma'abota girman kai.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky