Ayatullahi Imami Kashani Ya Ce: Shirin Raba Kasar Iraki Makircin Yahudawan Sahayoniyya Ne

Ayatullahi Imami Kashani Ya Ce: Shirin Raba Kasar Iraki Makircin Yahudawan Sahayoniyya Ne

Limamin da ya jagoranci sallar Juma'a a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Shirya zaben jin ra'ayin jama'a kan kokarin ballewar yankin Kurdawan Iraki daga kasar makircin yahudawan sahayoniyya ne

A hudubar sallarsa ta Juma'a a birnin Tehran: Ayatullahi Imami Kashani ya jaddada cewa: Dole ne Kurdawa su shirya daukan laifin raba kasar Iraki a tsawon tarihi, kamar yadda 'ya'yansu zasu dora musu laifin raba kasar a nan gaba saboda babbar laifi ne na cin amanar kasa.

Ayatullahi Imami Kashani ya kara da cewa: Kamata ya yi a ce mahukuntan yankin Kurdawan Iraki su kasance masu kishin kasarsu tare da kalubalantar shirin kasar Amurka da yahudawan sahayoniyya na samar da babban yankin gabas ta tsakiya ta hanyar raba kasashen yankin.

A gefe guda kuma Ayatullahi Imami Kashani ya bayyana bukukuwan makon tsaron kasa domin tunawa da yakin da kasar Iraki ta kallafawa kasar Iran da cewa yana da kima, kuma shi ne dalilin da ya sanya makiya suka fitar da rai daga cimma munanan manufofinsu kan kasar ta Iran.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky