Ayatollah Khamenei: Shaheed Hujaji Yana Da Matsayi Na Musamman

Ayatollah Khamenei: Shaheed Hujaji Yana Da Matsayi Na Musamman

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Sayyid Khamenei ya bayyana shaheed Muhsen Hujaji wanda ya yi shahada a hannun mayakan Daesh a kasar Siriya yana da matsayi na musamman a zukatan mutanen Iran, All.. ya daukaka shi a cikin shahidai masu kare harami

Jagoran ya bayyana haka ne safiyar yau Laraba a lokacinda ya ji kusa da gawar shahid Muhsen Hujaji wanda aka ajiye a masallacin Imam Husain (a) da ke cikin birnin Tehran. Jagoran ya kara da cewa, shahidai gaba daya suna da babban matsayin a wajen All... amma wasun All.. ta'ala yakan daukakasu akan wasu. Kamar dai yadda muke ganin yadda wannan shihidin ya shiga cikin zukatan ummar kasar Iran.

A yau Laraba ce za'a zagaya da gawar Shahid Muhsen Hujaji daga Masallacin Imam Husain (a) da ke nan Tehran zuwa dandalin shaheed duk a nan cikin Tehran 

Shahid Hujaji ya yi shahada ne a ranar 9 ga watan Agustan da ya gabata a lokacin da mayakan Daesh suka kama shi a kan iyakar kasar Syria da Iraqi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa hariman Sayyeda Zainab (a) dake birnin Demascus na kasar Syria.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky