Ayatollah Khamenei: Al Saud Masu Tsanani Ne A Kan Muminai Masu Rahama A Kan Kafurai

Ayatollah Khamenei: Al Saud Masu Tsanani Ne A Kan Muminai Masu Rahama A Kan Kafurai

Jagoran juyin juya halin muslucni a Iran ya bayyana mahukuntan kasar Saudiyya da cewa sun yi hannun riga da koyarwar kur'ani, inda suka zama masu cutar da muminai masu kyautatawa ga kafurai masu kiyayya da addinin muslunci.

Jagoran ya bayyana hakan ne a lokacin bude taron karatun kur'ani na shekara-shekara da ake gunarwa a gidansa a cikin watan azumin ramadan.

Ya ci gaba da cewa yin riko da koyarwar kur'ani mai tsarki shi ne mafita ga dukkanin matsalolin musulmi, amma abin ban takaici a yau an wayi gari mahukuntan kasar da aka safkar da kur'ani ita ce tafi kowace kasar musulmi mika kai kai ga makiya kur'ani da musulunci.

Ya kara da cewa Al Saud da ke rike da madafun iko a Saudiyya, sun zama wata saniya da Amurka ke tatsa, ta hanyar mika kudaden al'ummar kasar ga Amurka domin neman yardar mahukuntan kasar ta Amurka, wadanda kuma ba za su taba yarda da su ba, da zaran sun gama tatse su za su yi watsi da su.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda Al Saud suke kashe al'ummar musulmi a ko'ina ba tare da rahama ko jin kai ba, kamar yadda suke yi a Yemen, Bahrain da sauransu, amma kuma suna kaskantar da kai ga yahudawa da kafurai tare da mika dukiyar al'ummar kasar su gare su somin su kare su.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky