ANGUDANARDA TARON WAYARDA KAN IYAYE AKAN 'YA 'YANSU

ANGUDANARDA TARON WAYARDA KAN IYAYE AKAN 'YA 'YANSU

Kwamitin kula da tarbiyar yara matasa na harka islamiyya karkashin Jagorancin Sheikh Ibrahim Yaqoub Alzakzaky a yankin Sakkwato ya shirya tareda gabatarda taron wayarda kan iyayen yara na wuni daya dangane da tarbiyar 'ya 'yan nasu a karon farko. Taron wanda aka gabatar a jiya lahadi 17/06/2018 dai dai da 3/Sawwal, 1439. a Markazin 'yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub Alzakzaky dake Mabera Sakkwato.

Ya samu halartar bangaren biyu na iyayen yaran wanda ya hada 'yan uwa sisters da brathers, an kuma gabatar da muhimman batutuwa dangane da hakkokan da suka rataya ga iyaye akan 'ya 'yan nasu hadi da yanayin da tarbiyar yaran take ciki a halin yanzu, haka kuma an tabo batutuwa da yawan gaske dangane da makirce makircen yahudawa akan 'ya 'yan musulmi. Haka zalika taron ya samu halartar manya manyan Maluman da muke dasu a cikin wannan harka, wadanda suka hada da, Sayyid Ali Sidi, Malam Hashim Isah, Shekh Sidi Manir Sakkwato.

Rawar da kafafen sada zumunta ke takawa gurin gurbata tarbiyar matasa, Agent agent dinda yahudawa ke turowa a cikin harka domin lalata tarbiyar matasa, yadda za ayi a iya magance ire iren wadannan matsaloli da kuma karin shawarwari dangane da abinda ya shafi harkar Internet, ya ya kamata ayi amfani da hikima don isar da sakon harka. Na daga cikin batutuwan da aka wayar da kan iyayen yaran akansu.

sokoto

sokoto

sokoto

sokoto

sokoto

sokoto

sokoto

sokoto

sokoto


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky