?>

Ana yunkurin hallaka Sheikh Zakzaky

Ana yunkurin hallaka Sheikh Zakzaky

Shugaban dandalin yada labarai na harkar musulunci a Nigeriya,Ibrahim Musa ya fadi a wata takarda ta manema labarai da ya aiko da ita yau 19 ga watan 2017 cewa an yunkurin hallaka jagoran harkar musulunci a Nigeriya.Yana cewa:

“kamar yadda suka tsara,za a fara ta’addancin a kan IMN ne da zarar an yi wata muhimmiyar sanarwa mai matukar amfani a kwanaki kadan masu zuwa ko kuma makonni.Wadanda suka shirya makircin na son yin amfani da yanayin rashin tabbas da sanarwan zata haifar a siyasance wanda ya basu daman karasa mummunar manufarsu na kisan kiyashi da suka yi kuduri shekaru da dama,wanda ya bayyana karara a harin ta’addanci na shekarar 2015.Ta hanyar aikata mummunan kudirin nasu na kashe jagoranmu da kuma shekar da jinanain ‘yan kasa wadanda ba su ji,ba su gani ba,suna da borin kawo karshen harkar musulunci har abada.”
Sannan yayi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su tursasa gwamnatin tarayya ta tsawatar wa jami’an tsaron ta wanda kaman har yanzu basu gamsu da kaman rayuka kaman 100 da suka kashe a Zariya a watan Disambar 2015.
Ibrahim Musa ya tabbatar da cewa zasu cigaba da neman tabbatar da an yi masu adalci ga wadanda harin sojojin Nigeriya ya rutsa dasu a Disambar 2015 ta hanyoyin lumana kamar yadda suka saba.Sannan ya kara jaddada bugatarsu na a gaggauta sakin jagoransu  Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda kotu tayi umurni da sake shit un a watan disambar 2016


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*