Ana Gudanar Da Tarurrukan Juyayin Rasuwar Imam Khumaini (r.a) A Duk Fadin Iran

Ana Gudanar Da Tarurrukan Juyayin Rasuwar Imam Khumaini (r.a) A Duk Fadin Iran

A yau ne ake gudanar da bukukuwan juyayin rasuwar marigayi Imam Khumaini (r.a) wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci ta Iran a duk fadin kasar ta Iran inda ake sa ran a yammacin yau Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zai gabatar da jawabi kan hakan a hubbaren marigayi Imam din da ke wajen birnin Tehran

A wata sanarwa da cibiyar kula da kuma yada ayyukan marigayi Imam Khumaini (r.a) ta fitar ta ce za a gudanar da babban bikin juyayin tunawa da marigayi Imam Khumainin ne a hubbaren nasa a yammacin yau Lahadi da misalin karfe shida na yamma, sabanin yadda aka saba gabatarwa da safe saboda azumin watan Ramalana inda ta ce bikin juyayin na bana, kamar shekarun da suka gabata, za a gudanar da shi ne karkashin jagorancin  Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei wanda zai gabatar da jawabi a wajen.

Baya ga miliyoyin al'ummar Iran da suka hada da manyan jami'an kasar, har ila yau kuma taron zai sami halartar baki daga kasashe daban-daban na duniya bugu da kari kan 'yan jarida na ciki da wajen Iran.

A ranar 14 ga watan Khordad 1368 (wacce ta yi daidai da 4 ga watan Yunin 1989) ne Allah Yayi wa marigayi Imam Khumaini (r.a) rasuwa, shekaru 10 da nasarar da ya samu na jagorantar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran wanda ya fatattaki gwamnatin kama karya ta Shah a kasar. A duk shekara idan wannan rana ta zagayo al'ummar Iran suka gudanar da bukukuwan juyayin wannan babban rashi da aka yi da kuma sake jaddada mubaya'arsu a gare shi da kuma koyarwar da ya bari.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky