Ana Daf Da Kada Kuri'a A Babban Zaben Iran

Ana Daf Da Kada Kuri'a A Babban Zaben Iran

A yayin da ya rage 'yan sa'o'i kadan a fara kada kuri'a a babban zaben Jamhuriya musulinci ta Iran, ma'aikatar cikin gidan kasar ta ce ta shirya saf domin gudanar da zaben.

A gobe Juma'a ne al'ummar Iran ke kada kuri'a a zaben shugaban kasar gami dana wakilan jihohi da kuma na kauyuka. 

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta sanar da cewa za'a bayyana sakamakon zaben daki-daki maimakon ta gabadaya da aka sanar tunda farko.

Da misalin karfe takwas na safiyar wannan Alhamis ce wato karfe (3h30 na dare ogogon GMT) aka rufe yakin neman zaben.

'Yan takara hudu ne dai zasu fafata a zaben shugaban kasar karo na 12 tun bayan juyin juya halin musulinci na kasar da suka hada da shugaba mai barin gado Hassan Rohani daEbrahim Raïssi, da Mostafa Agha-Mirsalim, da kuma Mostafa Hashemi-Taba. 

Kafin hakan dai 'yan takara da suka hada da magajin birnin Tehran Mohammad-Baqer Qalibaf da kuma mataimakin shugaban kasar na farko Es'haq Jahangiri sun jange daga takarar zaben.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky