Ana Ci Gaba Da Yabawa Sojojin Da Suka Kwato Mosul A Iraki

 Ana Ci Gaba Da  Yabawa Sojojin Da Suka Kwato Mosul A Iraki

Duniya na ci gaba da jinjinawa da kuma yabawa sojojin Iraki da dukkan dakarun da suka taimaka wajen kwato birnin Mosul daga hannun 'yan ta'addan Da'esh

Sakon baya bayan nan shi ne na shugaba Emmanuel Macron na faransa wanda ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, Faransa tana jinjinawa sojojin Iraki da dukkan dakarun, ciki har da na kasarsa da suka taimakwa wajen kwato tsohon birnin na Mosul.

A jiya Lahadi ne firaministan Iraki ya ziyarci Mosul inda ya sanar da murkushe 'yan ta'addan daga birnin, bayan kwashe kusan watanni tara na fafatawa da kungiyar.

'Yantar da birnin Mosul dake zamen babban sansani na kungiyar IS a Iraki tun cikin shekara 2014, ita ce kawo yanzu wata babbar nasara da aka samu kan 'yan ta'addan na IS.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1441 / 2020
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni