?>

An yi taron tunawa da ranar Kudus ta duniya da kuma kaddamar da littafi a Abuja

An yi taron tunawa da ranar Kudus ta duniya da kuma kaddamar da littafi a Abuja

A yau Asabar,29 ga watan Yuli 2017,’yan harkar Musulunci a Nigeriya suka shirya taro na musamman domin tunawa da ranar Kudus ta duniya da kuma kaddamar da littafi a Abuja tarayyan Nigeriya.
An yi wannan taro ne dakin taro na Merit House dake Abuja.Bayan bude taro da addu’a ne,Dr Shu’aibu ya bayyana maqasudin taron da taken taron da kuma mutanen da zasu gabatar da kasida a wajen taron.
Hon.Ebenezer Oyintikin,daya daga cikin wa’yanda suka gabatar da kasida a wajen ya bayyana cewa shi kirista ne amma yana amfani da wani hadisi ya samu daga Annabi Muhammadu(sawa) cewa: “Idan abinda zaku saya ma ‘ya’yanku ba zasu isa ku raba ku hada da yaran makwabtanku ba,to,ku basu a cikin gida kar ku sake su fita dashi waje.”
Ya cigaba da cewa ya san Harkar Musulunci wadda Sheikh Zakzaky yake jagoranta ta doru ne akan wannan hadisi na Annabi da tsari na tausayi ga al’umma da jin kai.
Shi kuma Hon.Deji Adeyanju a nashi jawabin cewa yayi:
“Ban taba ganin lalatacciyar gwamnati kamar ta Nigeriya ba.Basa girmama mutanen kirki masu ilimi amma suna sasanci da lallaban ‘yan ta’adda.Na tabbata da shi’a suna da makamai da tuni gwamnati ta fara sasanci da su.
“Takurawar da gwamnati take maku ta kaikace tana fada maku ne ku dauki makamai ku zama ‘yan ta’adda,sai ku kuma kuka nuna masu kuna da hankali da tunani.”
Deji ya nuna takaicinsa dangane da lalacewan kasan nan,yana cewa:
“Ya gwamnati zata kashe mutum sama da 1000 amma shugaban kasa ya fito gidan talabijin yana cewa “me yasa suke dukan kirjin soja?”Wallahi baka da Kalmar da zaka iya fassara wannan gwamnati.”
Dr John Danfulani a lokacin da yake gabatar da nashi bayanin ya bayyana abubuwan alkairi da ya gani game da Harkar Musulunci a Nigeriya,yana cewa:
“Na halarci ayyukan da tarukan IMN da yawa fiye da yadda wani dan IMN din.Na je Tattakin Arba’een,na ga bayin Allah da aka kashe a lokacin tattakin,na ziyarci Sheikh Zakzaky lokaci daban daban.Na fahimci cewa ‘yan harka suna da tsari kuma suna tare da Allah.Ya za a yi cikin kasa da shekara 40 ya zama an iya samar da mutane sama da miliyan 20 in ba abin Allah ba?
“Kaman yanda na ga wani hadisi yana cewa shi mutum imma dan uwanka ne a halitta ko dan uwanka a addini.Kuma shi’a sun yi riko da wannan hadisin ta yanda suke mu’amala da kowa kamar yadda ya gabata.Har yanzu ba zaka taba samun dan shi’a dan ta’adda ba,dukkan bangarorin ISIS,DAESH da Boko Haram dukkansu ba shi’a bane.”
Daga cikin wa’yanda suka gabatar da kasida a wajen taron akwai;Professor Chidi Odunkalu,Alhaji Muktar Sirajo,da sauransu.
Sheikh Abdulhamid Bello ne ya wakilci Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a taron.Sannan da aka zo kaddamar da littafin da aka wallafa,sun sayi kofi biyu akan kudi naira dubu dari ga Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim.
Sannan Ahlul Dothour sun sayi kwafi 10 akan kudi naira dubu dari biyu,sai Malam Gamawa ya sayi kwafi 10 akan kudi naira dubu dari biyu da hamsin ga Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasiru ElRufa’I da Sufeto Janar na ‘yan sanda da sauransu.
Duk da ‘yan sanda sun kawo ziyara wajen sun tafi ba tare da wani abu ya faru ba,kuma an kammala taron lafiya cikin nasara.

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja

Abuja


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*