An Sanar Da Cafke Wasu 'Yan Ta'adda A Iran

An Cafke Wasu Yan Ta'adda Iran

An Sanar Da Cafke Wasu 'Yan Ta'adda A Iran

Jami'an tsaron Iran masu gadin iyakokin kasar sun samu nasarar cafke wasu gungun 'yan ta'adda a lardin Kermanshah da ke yammacin kasar

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, ma'aikatar harkokin cikin gidan Iran ta sanar da cewa, jami'an tsaron sun samu nasarar cafke 'yan ta'addan ne a kan iyakokin kasar da ke lardin na Kermanshah, bayan musayar wuta da aka yi, inda aka halaka biyu daga cikin 'yan ta'addan.

Bayanin ya ce an samu tarin makamai tare da su, da kuma wasu kayan sadarwa da suke dauke da bayanai dangane da shirin da suke da shi na kaddamar da hare-hare a cikin lardin na Kermanshah.

Haka nan kuma an samu wasu muhimman bayanai tattare da su, da ke tabbatar da cewa wasu kasashen larabawa 'yan amshin shatan Amurka ne suka turo su domin kai hare-hare a cikin kasar ta Iran.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky