An kashe Wasu jami'an 'yan sanda a Abuja

An kashe Wasu jami'an 'yan sanda a Abuja

Wasu ‘wadanda ake zargin yan fashi da makami ne sun kashe jami’an ‘yan sandan Najeriya bakwai a babban birnin kasar, Abuja.

Rahotanni na cewa lamarin ya auku ne a yammacin yau Talata a mahadar hanyar Galadimawa da ta ratsa hanyar filin jiragen sama na kasa da kasa.

Kwamishinan ‘yan sandan birnin Abuja, Sadiq Bello ya tabbatar wa manema labarai da aukuwar lamarin duk da cewa bai bada cikakken bayani ba.

Tuni aka kwashe gawarwakin 'yan sandan, yayin da mazauna yankin suka shiga halin firgici.

Bayanai na cewa, 'yan fashin da ke cikin mota sun far wa 'yan sandan ne cikin ba-zata a dai dai lokacin da suke bakin aiki.

Wannan na zuwa ne kwanaki uku da aka kashe wasu jami’an ‘yan sanda a Akwa Ibom da ke kudancin kasar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky