An Kama Mutane 48 Da Ke Da Alaka Da Harin Ta'addancin Tehran

An Kama Mutane 48 Da Ke Da Alaka Da Harin Ta'addancin Tehran

An Kama Mutane 48 Da Ke Da Alaka Da Harin Ta'addancin Tehran
A ci gaba da binciken da ake bayan harin ta'addancin Tehran wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 17, ma'aikatar tattara bayannan sirri ta Iran ta ce an cafke mutane 48 da ake zargi da hannu a jerin hare-haren na ranar Laraba data gabata.

Mutanen dai an cafke su ne tare da hadin kan iyalan 'yan ta'addan da suka kai hare-haren a yankuna biyar na kasar dake arewa maso yamma, da suka hada da Kermanshah, Kurdistan, Azerbaïjan da kuma Tehran babban birnin kasar.

A yayin samamen da jami'an tsaron kasar suka kai an kuma gano bindigogi masu da kayayakin hada boma-bomai da kuma damara masu fashewa.

A wani labari kuma an cafke wani mutum wanda ba dan kasar Iran ba ne a lardin Mahchahr na Khouzestan wanda a cewar labarin shi ne ke taimakawa 'yan ta'addan da kayan aiki.

A jiya ne dai akayi jana'izar mutane 17 da suka rasa rayukansu a jerin hare-haren ta'ddancin da aka kai a ranar 7 ga watan nan a majalisar dokoki da kuma hubbaren Iman Khomeini wanda ya asassa Jamhuriya musulinci ta Iran.

A halinda ake ciki dai gwamnatin Iran da al'ummarta na ci gaba da samun sakwannin ta'aziyya daga kasashen duniya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky