An Kai Harin Ta'addanci A Garin Ahvaz Iran

An Kai Harin Ta'addanci A Garin Ahvaz Iran

Wasu gungun 'yan ta'adda sun bude wuta kan jami'an tsaron Iran da fararen hula da suke gudanar da bikin makon tsaron kasa a garin Ahwaz da ke shiyar kudu maso yammacin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran "IRNA" a yau Asabar: Gwamnan jihar Khuzestan da ke kudu maso yammacin kasar Iran Ghulam Ridha Shari'ati ya bayyana cewa: A daidai lokacin da jami'an tsaron Iran ke gudanar da faretin soji a ranar bikin makon tsaron kasa da aka fara a yau Asabar a garin Ahwaz da ke jihar Khuzestan, wasu gungun 'yan ta'adda sun bude wuta kan mai uwa da wabi kan al'ummar da suke gudanar da bikin lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar mutane fiye da goma tare da jikkatan wani adadi mai yawa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa: A halin yanzu yawan mutanen da suka rasa rayukansu sun doshi 20 yayin da wadanda suka samu raunuka suka haura 60.

Ghulam Ridha Shari'ati ya bayyana cewa: Jami'an tsaron kasar ta Iran sun samu nasarar shawo kan matsalar tsaro a garin na Ahwaz, kuma tuni aka garzaya da mutanen da suka samu raunuka zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu. Kamar yadda wata majiya ta bayyana cewa: Jami'an tsaron Iran sun yi nasarar halaka 'yan ta'adda uku tare da kame guda daga cikinsu, kuma dukkaninsu 'yan yankin garin na Ahwaz ne da ke lardin Khuzestan


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky