An kaddamar da Hukumar Sintiri a Jihar Kaduna

An kaddamar da Hukumar Sintiri a Jihar Kaduna

Jawabin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a wurin Bukin Kaddamar da Hukumar Sintiri ta Jihar KadunaWannan hukuma an kirkire ta ne don a inganta tsaro a jihar, al’ummarmu su zauna cikin aminci a kokarin da suke yi don neman na kansu da iyalansu. An yi hukumar ne don ta taimaka wurin inganta tsaro a garuruwanmu da unguwanninmu.


Wannan yinkuri na kafa wannan hukuma, wani mataki ne na zuba jari wurin tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummarmu. Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna za ta taimaka wa sauran hukumomi na jami’an tsaro wadanda suke mallakkin Gwamnatin Tarayya ne.


Lura da irin fadin kasa da yawan al’ummar da muke da su a jihar tamu ta kaduna, muna iya cewa matsalar tsaro ita ce ta fi damun mu wadda ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi da dama saboda karancin jami’an tsaro na ‘yan-sanda da ake da su. Matsalar karancin ‘yan-sanda matsala ce ta kasar baki daya wadda miyagun mutane ke amfani da damar don cutar da al’umma. Saboda haka, maimakon mu rungume hannuwanmu muna jiran Gwamnatin Tarayya ta samu kudi ta dauki sababbin ‘yan sanda ko kuma jiran dokar da za ta ba jihohi damar yin nasu ‘yan sandan.  


Bisa wannan dalili ya sa a shekara ta 2016 , Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi dokar da ta ba ta damar kafa hukumar sintiri don taimaka wa ‘yan-sanda da sauran jami’an tsaro don magance matsalar ayyukan ta’addanci a garuruwanmu da unguwanninmu. Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna za ta yi aiki sau da kafa da Jam’an Tsaro na ‘Yan-Sanda da Sibiliyan Defens da kuma sojoji, musamman a wurin samar da bayanai na sirri.


Gwamnatin nan ta dukufa wirin ganin ta magance matsalar ‘yan sara-suka a unguwaninmu na birane da kuma ‘yan ta’addan da ke addabar mu a karkara. Jami’an tsaro sun kama wadannan ’yan sara-suka da dama kuma suna nan a tsare don fuskantar shari’a.


Wannan gwamnatin ba za ta bari wasu haramtattun kungiyoyi su yi amfani da wannan  dama da sunan tsaro su tayar da fitina ba. Zan so in yi amfani da wannan dama wurin ganin na sanar da jama’a cewa wannan Hukumar Sintiri  ta Jihar Kaduna doka ce ta kafa ta kuma ita daya ce kawai gwamnati ta san da ita. Saboda haka muna rokon al’umma su ba su hadin-kai.


Doka ba ta san da wata kungiya ta sintiri ba banda wannan. don haka muke sanar da al'ummar jahar kaduna, kungiyoyin sintiri kamar su: Kato da Gora, Civilian JTF, CESSCUR, Neighbourhood Watch, Vigilante Group of Nigeria, Extreme Security, Jarumai da Gora, Yan Committee, Ujumeme, Yan Tuba da sauransu duk haramtattu ne. Sannan ana kiran jami’an tsaro da cafke duk wani da zai fito yana amfani da sunan irin wadannan kungiyoyi. Su kuma kungiyoyin da mambobinsu ana kiran su da su zo su hada kai da Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna don ganin an magance tsaro a Jihar.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky