An Gudanar Da Taro Tsakanin Iran Da Manyan Kasashe Kan Yarjejeniyar Nukilya

An Gudanar Da Taro Tsakanin Iran Da Manyan Kasashe Kan Yarjejeniyar Nukilya

An gudanar da zaman taro na ministocin harkokin wajen manyan kasashe duniya da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya a birnin New York a gefen babban taron majalisar dinkin duniya a daren jiya.

Tashar Press TV ta bayar da rahoton cewa, ministocin harkokin wajen Iran da sauran manyan kasashen duniya da suka rattaba hannu kan yarjejeniya kan shirin Iran na nukiliya, sun sake cimma wata matsaya a jiya a birnin New York, kan wajabcin ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar nukiliya, tare da kare ta.

Bayan kammala zaman taron, babbar jami'a mai kula harkokin siyasar wajen tarayyar turai Federica Mogherini, tare da ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif, sun gudanar da taron manema labarai.

Fedirica Mogherini ta bayyana cewa za su samar da wani tsari nan da za su yi amfani da shi wajen mu'amalar kudade tare da Iran, kamar yadda shio ma Zarif ya yaba da shirin da kum ajadda wajabcin cika dukkanin alkawullan da dukkanin bangarorin yarjejeniyar suka dauka.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Arba'een
mourning-of-imam-hussain
پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky