An gudanar da Muzaharan Free Zakzaky a babban birnin tarayya Abuja

An gudanar da Muzaharan Free Zakzaky a babban birnin tarayya Abuja

An gudanar da Muzaharan Free Zakzaky a babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda aka saba kullum dakarun Matasa yan Abuja Struggle, na gabatar da Zan-Zanga ta lumana na kiran gwamnatin Nigeria ta saki, Jagoran Harkar Musulunci Sayyid Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa dan kulawa da lafiyarsa

  Muzaharan yau ta taso ne daga Filin yanci dake Unity Fountaine, ana tafe ana fadin "Free Zakzaky for need a good doctor, aka kamo hanyar Federal Secretariat dake babban birnin tarayya, daga isowar Muzaharan Eagle Square ta zarce ta shiga majalisar ƙasa dake gabas da Eagle Square.

Dakarun Matasa da Sister's cikin tsari da nizami suke tafiya, cikin sahu rike da poster na Jagora Sayyid Zakzaky (H), da mai dakinsa Sayyida Zeenatuddeen ana fadin Free Zakzaky Free Zeenatuddeen for need a Good Doctor, haka Muzahara ta cigaba da tafiya har ta iso bakin get na Majalisa, kafin shigar wannan Muzahara din kan hanyar majalisa.

   Jami'an yan sanda sun so hana yan uwa shiga wannan wuri din, amman cikin ikon Allah lami Lafiya aka shiga aka tsaya bakin get din, inda ana aka gabatar da jawabai daga bakin Mrs Deji Adeyanju, daku kuma wani dan kabilar Ibo daga bisani kuma aka mika abin magana ga Engineer Abdullahi, shima ya gabatar da jawabi sannan aka baiwa mawaka suma suka gabatar da wake na juyayi.

An gabatar da sallan Azahar da la'asar dukka a wurin, sannan aka mika abin magana ga wakilin yan uwa na garin Gombe, Malam Muhammad Abbari ya gabatar da Engineer Abdullahi, ya isarwa yan uwa sakon da yazo musu daga wurin wa'annan mutane din yan majalisu, bayan kammala jawabin Engineer Abdullahi Acadamic Forum sai aka mika abin magana ga mai rufe wannan Muzahara din da jawabi, Sheikh Sunusi Abdulkadir Kano.*l

Bayan jawabin rufewa da Sheikh Sunusi Abdulkadir Kano yayi, sannan Malam Abubakar Abu-Sumayyah Gwagwalada ya rufe da Addu'a.
    Anyi Muzahara lafiya an tashi lafiya, abinda ke biyo baya hotunan yadda Muzaharan ya gudanane, da zaman dirshan na gaban majalisan tarrayya Abuja Nigeria.


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky